Kungiyar Kwadago A Najeriya Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

Hadaddiyar Kungiyar Kwadago A Najeriya Ta Shiga Yajin Aiki

Hadaddiyar kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC da TUC ta ayyana tsunduma gagarumin yajin aiki daga ranar Talatar nan ne har sai baba ta gani.

Matakin yajin dai don nuna fushi ne da lakadawa shugaban kungiyar kwadagon Komred Joe Ajaero duka a jihar Imo a gangamin nemawa ma'aikata hakkinsu.

Hadaddiyar Kungiyar Kwadago A Najeriya Ta Shiga Yajin Aiki

Bayan taron hadaddiyar kungiyar kwadagon a Abuja, jagorori sun umurci ma'aikata a duk fadin Najeriya su auka yajin aiki don neman lalle a takawa gwamnan Imo Hope Uzodinma birki kan zargin tura 'yan sanda da 'yan sara suka wajen cin zarafin Ajaero da wasu mukarraban sa.

‘Yan kwadagon sun ce da gangan gwamnati ta ki daukar mataki kuma ai ‘yan sanda jami’an gwamnatin tarayya ne.

Rundunar 'yan sanda Najeriya ta ce ta kaddamar da bincike kan zargin da aka yi cewa har da jami'anta a zargin cin zarafin Ajaero.

Babban sakataren kungiyar kwadago ta TUC Komred Nuhu Toro ya ce sam ba za su ci gaba da lamuntar dirar mikiya a kan 'yan kwadago daga 'yan siyasa irin Hope Uzodinma ba.

Hadaddiyar Kungiyar Kwadago A Najeriya Ta Shiga Yajin Aiki

Shi ma sakataren tsare-tsare na NLC Komred Nasir Kabir ya ce Uzodinma na neman maida Imo wata jiha mai hatsari.

Duk da Uzodinma ya nemi afuwar fashin albasa da jami'ai suka yi wa Ajaero da nuna bai san ya shigo jihar Imo ba, 'yan kwadagon sun ayyana gwamnan da cewa ba za a amince da irin siyasarsa ta banga ba.

Kungiyar Kwadago A Najeriya Ta Shiga Yajin Aiki

Uzodinma ya yi nasarar lashe zaben tazarce a karshen mako inda ba mamaki hakan ya taimaka wajen rage caccakar shi da cewa gwamna ne nadin kotun koli.

Yanzu za a jira irin martanin da fadar Aso Rock za ta fitar kan matakin ‘yan kwadagon.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Hadaddiyar Kungiyar Kwadago A Najeriya Ta Shiga Yajin Aiki Har Sai Masha Allah.mp3