Haaland ya fita atisaye da sauran abokan wasansa na City gabanin karawar da kungiyar za ta yi da Young Boys a gasar Zakarun Turai a ranar Talata.
Washington D.C. —
Manajan Manchester City Pep Guardiola, ya ce dan wasansa Erling Haaland ya samu sauki bayan da ya gurde kafarsa a karshen makon da ya gabata.
Haaland ya fita atisaye da sauran abokan wasansa na City gabanin karawar da kungiyar za ta yi da Young Boys a gasar Zakarun Turai a ranar Talata.
An dai cire Haaland a lokacin hutun rabin lokaci a karawar da City ta yi da Bournemouth wacce ta lallasa 6-1 a ranar Asabar bayan da ya gurde a kafa.
Guardiola ya ce an cire Haaland a wasan ne bayan da ya ce ba ya jin dadi.
“Na gana da likitan da shi kansa Haaland, ya ce min ya samu sauki.” Guardiola.