Sanatar da tawagarta da suka hada da ‘yan jarida goma sha uku da direbansu, sun tsallake rijiya da baya ne bayan wasu matasa sun tare su a kan hanyarsu da dawowa Jos, jim kadan da kammala kaddamar da cibiyar sarrafa bayanai da fasahar sadarwa da dakin karatu na zamani, a garin Namu dake karamar hukumar Quan’Pan a jahar Filato.
Bayanai na nuni da cewa, kafin aukuwar lamarin, jami’an tsaro sun cafke wasu mutane hudu da suke zarginsu da safarar makamai, lamarin da ya sa matasan suka bukaci sanatan ta sa baki a sake su.
Wakilin jaridar Leadership a jahar Filato, Mr Achor Abimaje sun fuskanci barazana ga rayuwarsu daga wurin matasan.
Ku Duba Wannan Ma An Gudanar Da Bikin Ranar Yafiya A Jihar FilatoShima wakilin jaridar New Telegraph, Pam Musa yace sun yi tafiyar kilomita fiye da goma kafin suka sami taimako, bayan matasan sun kona motarsu kurmus.
Shugaban kungiyar wakilan gidajen jaridu na ‘yan korasfonda, Gyang Bere yace kamata yayi hukumomi su samarwa ‘yan jarida kariya, la’akari da irin gudunmuwa da suke bayarwa wajen hadin kai da ci gaban kasa.
Tuni dai shugaban kungiyar ‘yan jarida a jahar Filato, Mr Paul Jatau ya bukaci gwamnati ta zakulo wadanda suka kai harin don hukantasu da zamowa izina ga masu niyyar yin hakan.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5