Al’ummomin dake zaman doya da manja a wasu sassan jihar Filato, sun kara jaddada aniyarsu ta yafe wa juna da tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu.
Ranar bakwai ga watan Febrairun kowace shekara ne gwamnatin jihar Filato ta ayyana a matsayin ranar yafiya wa juna kan kashe-kashe da barnata dukiyoyi da a baya aka yi a jihar ta Filato wacce ka tsakiyar arewacin Najeriya.
Bikin na bana ya janyo al’ummomin jihar ne da dama daga sassa daban-daban da suka rika bayyana irin matakan da suka dauka na yafewa juna da inganata zaman lafiya.
Karamar hukumar Barikin Ladi da a shekarun baya take kan gaba wajen yankunan da ake samun tashin hankali, yanzu an samu daidaituwa kamar yadda Muhammad Adam Muhammad da Laurence Rondon suka bayyana.
“Yau dai ranar da ake gani musamman na yafiya ne, amma ko wacce rana ta zamanto cewa ranar yafiya ne”. A cewar Muhammad Adam.
“Gaskiya mun samu zaman lafiya a Barikin Ladi, muna sake godiya ga Plateau Peace Agency kuma. Zuwan su Barikin Ladi ya sanya muka kafa kungiyar Inter Faith, A wannan kungiyar muna zama ko wani wata mu tattauna matsalolin mu da suke kauyuka da yadda za mu magance su”. A cewar Laurence.
Gwaman jihar Filaton Simon Lalong ya yi alkawarin aiwatar da bukatun al’ummar.
An gudanar da bikin yafiyar a lambun yafiya dake tsakiyar birnin Jos.