Gwamtani Kaduna Ta Ce 'Yan Ta'adda Ne Suka Dasa Bama-bamai a Kabala

Jami'in yada labarai da hulda da jama'a na gwamnmatin jihar Kaduna, Samuel Aruwan

Gwamnatin jahar Kaduna ta ce an auna arziki ne da bama-baman da aka gano an dasa a yankin Kabala-West da Unguwan Romi ba su tashi cikin jama'a ba, amma da an yi asarar rayuka da dukiyoyi.

A maraicen ranar Lahadin da ta gabata ne dai wasu abubuwa da ake zargin bama-bamai ne su ka fashe a yankin Kabala-West da ke Karamar hukumar Kaduna ta Kudu kana daga bisani aka sake gano wasu abubuwan fashewar a yankin Unguwan Romi sai dai an auna arziki saboda ba a yi asarar rayuka ba.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya ce gwamnatin jihar ta fitar da tsare-tsaren magance wannan matsala baki daya.

Tuni dai masana harkokin tsaro a Najeriya su ka fara nazarin wannan sabuwar matsala da ta fito a Kaduna. Manjo Yahaya Shinko mai ritaya ya ce akwai wasu abubuwan lura.

Wannan dai shine na farko tun bayan zaben wannan gwamnati ta jahar Kaduna a shekarar 2015 da aka sami fashe-fashen da gwamnatin ke ganin 'yan-ta'adda ne sanadi, saboda fashewar baya da aka taba samu a yankin sabon Tasha na masu sana'ar kayan da ke da nasaba da fashewar ne.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamtani Kaduna Ta Ce 'Yan Ta'adda Ne Suka Dasa Bama-bamai a Kabala