A daidai lokacin da jami'an tsaro da wasu gwamnatoci ke nuna damuwa game da masu baiwa 'yan-bindiga bayanan sirri, muryar wata mata da ta karade shafukan sada zumunta inda ta zargi wani direba a tashar Kawo da hada baki don mika ta da 'yan uwanta bakwai ga masu sace mutane ya sa hukumomi sun kaddamar da bincike
Ko da yake, shugabanni direbobi a tashar ta Kawo sun musanta wannan mata inda har suka nemi da ta je ta ba da sheda.
Jahar Kaduna dai na cikin jihohin Najeriya da ke fama da hare-haren 'yan bindiga da kuma sace mutane wanda wannan ne ya sa muryar matar da aka fara yawo da ita a kafafen sada zumunta na zamani a farkon makon nan, ta ja hankalin mutane da dama.
Matar wadda ba ta bayyana sunan ta ba, ta ce da kyar su ka tsira.
Tuni dai wannan murya ta kai kunnen mahukunta kuma har ma wasu daga cikinsu sun ziyarci tashar ta Kawo don bibiyar batun kuma Sakataren kungiyar direbobi ta NURTW, Kwamared Bature Yusuf Suleman ya nuna shakku kana bayanan matar inda ya ce akwai tsarin da suke bi wajen yin lodi a tashar.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna CP Mudashiru Abdullahi dai ya ce su na binchike game da wannan zargi.
Da yawan matafiya dai kan shiga tashoshin mota ne don gujewa tarkon mabarnata kuma wannan ne ya sa zargin wannan mata na hadin baki da direban motar da su ka shigo daga tasha ya ja hankalin mutane da dama.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna: