Gwamnoni Sun Mikawa Zabebben Shugaban kasa Sunayen Ministoci

Kan maganar cewa wasu gwamnoni sun mikawa zabebben shugaban kasar Najeriya jerin sunayen ministocin da suke son ya nada, ana kuma rade-radin cewa ya gwale su.

A dalilin haka ne ya kai ga tambayar shin menene Kudurin dokar tsarin mulkin Najeriya ta tanadarwa shugaban kasa wajen nada ministocin sa? Tambayar kenan da Hajiya Jummai Ali tayi wa babban lauyan tsarin mulki Hassan Liman.

Hassan Liman yace in aka duba cikin tsarin mulkin Najeriya kashi na ‘dari ‘daya da arba’in da bakwai ‘karamin kashi na ‘daya ance zabebben shugaban kasa shine zai ce ga adadin ministoci da zai nada a tarayyar Najeriya, ya kuma kamata a karkashin dokar kashi na ‘daya idan ya tashi nada ministocin da ya tabbatar da ya samu mutum ‘daya daga duk jihohin kasar baki domin tsarin mulki ne ya tanadi haka.

Kamar yadda a dokar tsarin mulkin Najeriya aka ce gwamnoni sune kadai ke da ikon nada kwamishinonin su, haka shima shugaban kasa yana da karfin mulkin yin hakan.

Amma yana da kyau zababben shugaba ya ‘dauki shawarar mutanen da suka ‘daura shi matsayinsa na shugaba ba laifi bane.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnoni Sun Mikawa Zabebben Shugaban kasa Sunayen Ministoci - 2'13"