Shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su, da kuma gwamnatin jihar Borno a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi ta hannun mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale.
“Shugaba Tinubu ya bayyana hare-haren a matsayin ta’addanci da ya nuna irin matsin lambar da ‘yan ta’adda ke fuskanta da kuma nasarar da aka samu wajen rage karfinsu na kaddamar da hare-hare."
Shugaba Tinubu ya kara da cewa, "masu tayar da hankali zasu gamu da mummunar makoma kuma wadannan hare-haren matsorata ne kawai da ba zasu iya maida hannun agogo a baya ba, saboda gwamnatinsa ba za ta bar al’umma ta koma zamanin fargaba da hawaye, da bakin ciki, da zubar da jini ba.”
Ya kuma bada tabbacin cewa, gwamnatinsa na daukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron ‘yan kasa, tare da jaddada cewa, za a kara zage damtse wajen ganin an kawar da wadanda ke addabar al’umma da katse wa mutane hanzari.
A halin da ake ciki kuma, gwamnatin Amurka ta yi Allah wadai da harin da ta bayyana a matsayin rashin Imani.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, gwamnatin Amurkan ta hannun ofishinta a Najeriya, ta jaddada aniyar ta na hada kai da gwamnatin Najeriya domin murkushe ayyukan ta'addanci da kuma hukunta miyagu.
Sanarwar ta kara da cewa, “Amurka ta yi Allah wadai da munanan hare-haren da aka kai a Gwoza, jihar Borno a ranar 29 ga watan Yuni. Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalai da abokan wadanda aka kashe, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun cikakkiyar lafiya. Wannan munanan hare-haren manuniya ce ta irin barazanar da ta'addanci ke yi a yankin.”
Akalla mutane 18 ne suka mutu a ranar Asabar, sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon hare-haren kunar bakin wake da aka kai a garin Gwoza na jihar Borno
Hukumomi a jihar Borno sun bayyana jiya lahadi cewa, wadansu mata uku ‘yan kunar bakin wake sun kai hari a wajen wani bikin aure, da wurin jana’iza, da kuma asibiti suka kashe akalla mutane 18.
Kawo yanzu, babu kungiyar da ta dauki alhakin hare-haren.
Ku Duba Wannan Ma An Tabbatar Da Masu Juna Biyu Na Cikin Mutum 18 Da Suka Mutu A Harin Jiya Asabar A Borno