Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tabbatar Da Masu Juna Biyu Na Cikin Mutum 18 Da Suka Mutu A Harin Jiya Asabar A Borno


Harin Boko Haram
Harin Boko Haram

An kasha akalla mutane 18, yayin da wasu 30 suka jikkata bayan wasu jerin hare-haren da ake zargin wasu mata ‘yan kunar bakin wake ne suka kai a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya a jiya Asabar, in ji shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta yankin.

Borno dai na cikin shekaru 15 na hare-haren masu ikirarin kishin Islama wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da raba wasu miliyoyi da humallan su.

Duk da cewa sojojin Najeriya sun rage karfin mayakan, amma har yanzu suna kai munanan hare-hare kan fararen hula da kuma wuraren tsaro.

Barkindo Saidu, shine babban Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno, ya ce wasu da ake zargin 'yan kunar bakin wake ne suka kai hari daban-daban a wajen bikin aure da jana'iza da kuma asibiti, inda suka kashe mutane tare da jikkata wasu da dama a garin Gwoza.

Saidu ya ce an tabbatar da mutuwar mutum 18, adadin da ya hada da kananan yara da manya da ma mata masu juna biyu.

Sai dai babu wata kungiyar ko wani mutun da ya dauki alhakin kai wannan harin.

Boko Haram da ISWAP da ta balle kanta, su ne kungiyoyin ‘yan bindiga da suka fi yawan gudanar da ayyukan su a jihar Borno, wani babban yanki na karkara mai girman gaske.

Ga dai karin bayani cikin sauti a rahoton Ibrahim Mustapha:

An Tabbatar Da Mutuwar Mutum 18 A Harin Da Aka Kai A Gwoza.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG