A ci gaba da kokarin kawo karshen ta’addancin ‘yan kungiyar Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya, dakarun rundunar “Operation Lafiya Dole” sun ci gaba da kai farmaki a sansanoni daban-daban na mayakan Boko Haram.
Dakarun babban sansanin sojoji na goma sha daya dake Gamboru sun ceto wani dattijo da ‘yan ta'addan suka sace, lokacin da dakarun suka durfafo, ‘yan ta'addan sun bar wannan dattijo da ma makamansu.
Ka zalika sojojin sun kaddamar da wani mummunan farmaki akan sansanin Boko haram dake Gava a yankin karamar hukumar Gwoza, inda suka kashe yan ta'adda goma sha biyar tare da raunata wasu da dama.
Amma kamar yadda babban jami'in samar da bayanai a hedkwatar rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar John Enenche ya sanar, a wannan farmaki an gano wata mata da ‘yan ta'addan suka sace shekaru biyar da suka gabata bayan da suka kashe mijinta. Ya ce, amma a halin yanzu tana nan sun kaita asibiti ana kulawa da ita.
Sai dai duk da wannan hobbasa da dakarun suke, inji Janar Enenche, wasu ‘yan tsiraru ‘yan ta’addan suna kawo cikas a wannan yaki, domin an cafke wani mai suna Bakura Rawa Modu a sansanin ‘yan gudun hijira dake Dalori da yake wa mayakan na boko haram leken asiri.
Binciken ya tabbatar da shi akai ta kitsa kai hare-haren kunar bakin wake a yankunan konduga, sannan ya kuma taka rawa a hare-haren da Book Haram tai ta kaiwa akan sojoji da fararen hula a shekaru biyar da suka gabata.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum