Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Ibrahim Dosara.
Sanarwar ta kara da cewa “Majalisar tsaro ta jihar Zamfara ta amince tare da bayar da umarnin rufe wasu kafafen yada labarai a jihar saboda karya dokokin aikin jarida,”
Kafofin yada labaran da abin ya shafa sun hada da Rediyon Najeriya, Pride FM Gusau, NTA Gusau, Gidan Talabijin na Gamji, Vision FM, da Al Umma TV.
A cewar sanarwar, gwamnatin ta kuma umurci kwamishinan ‘yan sanda na jihar da ya kamo duk ‘yan jarida da suka halarci taron da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Dr Dauda Lawal Dare ya shirya. “An ba da umarni ga kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara da ya kama duk wanda ya yi watsi da wannan umarni."
A baya dai gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da dakatar da duk wasu harkokin siyasa da kuma wasu sabbin matakan tsaro a jihar saboda tabarbarewar tsaro.
Sai dai duk da haka, PDP ta shirya taron a ranar Asabar da zimmar karɓar wasu 'yan adawa da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar tasu, lamarin da ya kai ga hatsniya tsakanin wasu magoya bayan jam’iyyar PDP da na APC a jihar.