Gwamnatin Yobe Ta Ce Ta Kawar Da Cutar Amai da Gudawa

Dr. Muhammad Bello Kawuwa kwamishanan kiwon lafiya na jihar Yobe

Kwamishanan kiwon lafiya na jihar Yobe Dr Kawuwa ya tabbatar cewa yanzu babu cutar amai da gudawa a jiha saboda bayan kwanaki 21 babu inda ta sake bullowa

Gwamnatin jihar Yobe ta ce ta kawo karshen matsalar cutar amai da gudawa da ta barke a wasu sassan jihar.

Cutar ta yi sanadiyar mutuwar mutane 16 cikin wasu mutane 404 a kananan hukumomi da suka kamu da cutar.

Tun ranar 24 na watan Maris din wannan shekarar aka samu bullar cutar a jihar inda aka ce mutane 34 suka kamu da cutar a karamar hukumar Gashua inda nan take mutane biyar suka halaka. Daga bisani kuma an samu yaduwar cutar zuwa wasu Kananan hukumomi.

Kwamishanan kiwon lafiya na jihar Dr. Muhammad Bello Kawuwa y ace yanzu babu cutar a jihar saboda an kwashe fiye da kwanaki 21 babu labarin bullar cutar a koina. Y ace gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki sun yi duk abun da ya dace.

A tsarin hukumar kiwon lafiya ta duniya kamar yadda kwamishanan ya fada bayan kwanaki 21 ba’a samu bullar cutar ba, an shawo kanta ke nan.

Dr Kawuwa y ace sun shiga lungu lungu, da gidaje suna fadakar da mutane abun da yakamata su yi domin gujewa kamuwa da cutar.

Haruna Dauda nada karin bayani a wannan rahoton

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Yobe Ta Ce Ta Shawo Kan Cutar Amai da Gudawa - 3' 17"