Gwamnatin Trump Ta Kare Kamen Bakin Hauren Da Ta Yi

Mukaddashin shugaban hukumar tsaron cikin gidan Amurka, jiya Lahadi ya karesamamen da jami’an hukumar su ka kai a wasu masana’antun sarrafa abinci a Mississippi da zummar neman daruruwan bakin hauren da basu da takardun izinin zaman kasa, amma kuma ya amsa cewa lokacin da aka aka kai samamen bai dace ba, saboda 'yan kwanaki kalilan ne kawai bayan da wani mahari ya auna kuma ya kashe ‘yan Hisfaniyawa 22 a wani harin harbin kan mai uwa da wabi a El Paso na jahar Texas.

Kevin McAleenan ya fada wa shirin gidan talabijin din NBC mai suna 'Meet the Press' cewa daga cikin mutane 680 da aka kama a samamen da aka kai kamfanonin biyar, dari biyu daga cikin sun aikata manyan laifuka don haka za a tasa keyarsu zuwa kasashensu na haihuwa.

Wasu hotunan telbijin sun nuna kananan yara na kuka a lokacin da aka kama iyayensu aka kuma tsaresu a cikin samamen, kuma ba za su iya dauko su daga makaranta ba yayin da aka kammala karatu a ranar Larabar da ta wuce.

Ya ce an sake mutane 32 daga cikin bakin hauren cikin awa guda kana aka sake 270 a cikin wuni guda, galibi saboda kula da ‘ya’yansu.