Tun a baya dai aikace aikacen kamfanonin Mai na kasashen waje a yankin Niger Delta, ke ci gaba da yin illa ga muhalli a Najeriya. Ministan muhalli ta Najeriya Hajiya Amina Mohammed, tace yanzu gwamnatin tarayya zata aiwatar da wani rahotan da tuni aka gabatar don kawo gyara.
Ministan muhalli tace alkawarin da shugaba Buhari yayi tun kafin hawa kujerar mulki, shine kan cewa wannan rahotan da akayi mai suna UNEP wanda aka yi shekaru 6 da suka gabata, ya kunshi masalaha kan yadda za a gyara muhallin da kamfanonin Mai suka gurbata.
Domin jin yadda girman matsalar take wakilin Muryar Amurka, Hassan Maina Kaina, ya nemi jin ta bakin Farfesa Alasan Mamman Mohammed na jami’ar Abuja, wanda yake kwararre kan muhalli. Farfesa Alasan yace “Kasan shi iskar gas da Man fetur suna haduwa ne guri guda, to kafin a samu Man fetur to dole sai an kona iskar gas din sannan a samu man fetur.” Ya ci gaba da cewa a Najeriya sai an kona iskar gas din amma a kasashen Turai doka ce kan kon iskar gas domin yana gurbata muhalli.
Tuni dai masana a Najeriya ke maraba da wannan mataki na gwamnatin tarayya, kamar yadda Injiniya Mohammed Kyari, yace da alama idan har gwamnatin Najeriya zata aiwatar da irin wannan rahoto to zata taimaka matuka ga lalacewar muhalli a yankin.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5