Gwamnatin Tarayya Ta Sake Barazanar Kama Masu Takardun Digirin Bogi

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewar hukumomin tsaro zasu fara farautar mutanen dake rike da takardun kammala karatun digiri na bogi a fadin Najeriya.

Ministan Ilimi Tahir Mamman ne ya bayyana hakan a Abuja a Talatar data gabata yayin karon farko na taron watanni uku-uku na 'yan kasa da masu ruwa da tsaki a bangaren ilmin Najeriya.

Ministan ya kuma baiwa 'yan Najeriya tabbacin gudanar da muhimman sauye-sauye a bangaren ilmi ta hanyar kaddamar da wata taswira mai fannoni 13.

Ya kara da cewar, matukar ana son gudanar da cikakken tsari a fannin ilmi, musamman a matakin firamare da karamar sakandare, ya zama wajibi a samar da sahihan bayanai da zasu bunkasa koyon sana'o'in dogaro da kai da zasu taimaka wajen rage yawan yaran da basa zuwa makaranta.

A farkon watan Janairun daya gabata, Ministan ya bayyana cewar hukumomin tsaro zasu fara farautar 'yan Najeriyar dake rike da takardun kammala karatun digirin bogi daga kasashen ketare dake amfani dasu wajen samun damammaki a kasar.

Tahir Mamman ya bayyana irin wadannan mutane da masu laifi. "bana tausayin irin wadannan mutane. a maimakon haka ma ina yi musu kallon wani bangare na gungun masu laifi daya kamata a kama".

Ministan Ilmin ya kara da cewar, gwamnatin tarayya zata dakatar da amincewa da takardun kammala karatun digiri daga karin kasashe irinsu; Uganda da Kenya da Jamhuriyar Nijar.