Gwamnatin Sokoto Ta Sha Alwashin Bin Kadin Marainiyar Da Maza Bakwai Suka Yi wa Fyade

Gwamnati jihar Sokoto ta dauki mataki akan wasu mutanen da ake zargi da yi wa wata yarinya fyade bayan kusan shekara guda da faruwar lamarin.

Bayan da rubdugun da kafafen yada labarai da kungiyoyin kare ‘yancin bil’adama suka yi wa gwamnatin jihar Sokoto akan korafin da wata mata ta yi cewa, magidanta bakwai sun yi wa diyar ta marainiya fyaden karba-in-karba kuma ba’a yi musu komai ba, duk da yake an gurfanar da su gaban kuliya, yanzu gwamnatin ta fito fili ta fadi matakin da ta dauka.

A ranar 19 ga watan Nuwamba na shekarar 2020, Sashen Hausa na Muryar Amurka ya bayar da labarin korafin cewa magidanta 7 sun yi wa wata marainiya 'yar shekara 12 fyaden karba-in-karba a Sokoto, daga nan kafafen yada labarai da kungiyoyin kare ‘yancin bil'adama suka shiga bibiyar wannan lamarin.

Da farko dai manema labarai sun nemi jin ta bakin gwamnatin jihar Sokoto akan korafin, amma abin ya ci tura, sai ga shi bayan matsin lamba akan batun, gwamnatin ta fito ta fadi matsayinta.

Baban lauyan gwamnati kuma baban lauyan Najeriya Sulaiman Usman ya ce, a ranar 11 ga watan Nuwamba 2020 fayil din wannan shari'ar ya iso ofishin sa, kuma kai tsaye ya sa masa hannu, kuma ya ba da umarnin cewa a dauki matakin da ya dace.

Lauya Sulaiman Usman ya ce, da yake kotun farko ta bayar da belin mutanen da ake tuhuma bisa la'akari da yanayin annobar cutar Coronavirus da bukatar rage cunkoso a gidajen yari, to dole yanzu sai sun dauki matakai na ganin an gurfanar da mutanen da ake zargi a gaban kotu, kafin a ci gaba da shari’ar. Kuma za su tabbata an bi kadin shari’ar.

Wakilin Muryar Amurka ya tuntubi mahaifiyar yarinyar, wadda ta yi korafin, akan ko yaya ta ke ganin matakin da gwamnati ta dauka? Inda ta ce, ba za ta samu nutsuwa ba, har sai an gurfanar da wadanda ake zargi, kuma an yanke musu hukuncin da ya dace.

Kungiyar kare ‘yancin bil'adama ta “Human Rights Network Nigeria” tana cikin kungiyoyin da ke bibiyar wannan lamarin, shugaban kungiyar a jihar Sokoto Sirajo Madawaki ya ce, wannan matakin da gwamnati ta dauka ya yi daidai.

Da yake yanzu shekara daya da faruwar lamarin, kuma ana ganin cewa ba'a yi komai ba, jama'a za su so su saka ido su ga wa'adin da wannan shari'ar da aka sake sakawa zai dauka, domin gwamnati na alfahari da cewa, sashen shari'ar ta yana cikin masu gudanar da hukunce-hukunce cikin hanzari.

Ga rahoton Muhammad Nasir ta sauti: