Gwamnatin Nijar Ta Kwace Ikon Gudanar Da Kamfanin Orano Na Faransa

Sojojin mulkin Jamhuriyar Nijar

A cikin wata sanarwa da kamfanin Orano mallakin kasar Faransa ya fitar a ranar Laraba da ta gabata ne, ya sanar da kwace ikon gudanar da tasharsa ta makamashin Uranuim dake jihar Agadez a Arewacin Nijar

Sabuwar takaddamar dai na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin mulkin sojin kasar Nijar ta baza jami’an tsaro a cikin kamfanin na Somair wanda Orano ke da sama da kaso 63 cikin 100 na hannun jarinsa.

Wannan matakin ya biyo bayan dakatar da aikin hako Uranuim a karshen watan Oktoban da ya gabata saboda rashin fitar da shi a kasuwannin duniya domin sayarwa sakamakon rufe iyakar Benin da Nijar.

Tuni gwamnatin Nijar ta fara zawarcin kasar Rasha domin ta zo ta zuba hannun jarin aikin hako Uranuim a kasar domin ta maye gurbin kasar Faransa.

To sai dai kanfanin Orano ya sanar da bin hanyoyin shari’a a kotun kasa da kasa domin neman hakkokin sa.

Matakin ya haifar da muhawara a tsakanin ‘yan kasar inda wasu ke ganin hakan ya dace yayin da wasu na ganin akasin haka.

Kungiyar dake sa’ido kan yadda ake hako arzikin karkashin kasa a Nijar ta bakin Ilyasu Bubakar ta bukaci gwamnatin Nijar da ta samar da hujjoji masu karfi wanda za ta iya kare kanta a gaban kotunan.

Malam Mohamed Jibril mai sharhi kan al’amuran yau da kullum na ganin akwai bukatar bangarorin biyu su bi hanyoyin tattaunawa domin warware takaddamar cikin lumana.

Yanzu haka dai ‘yan Nijar sun zuba ido su ga yadda za ta kasance tsakanin gwamnatin kasar da kuma kamfanin Orano na kasar Faransa

Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Nijar Ta Kwace Ikon Gudanar Da Kamfanin Orano Na Faransa.mp3