Gwamnatin Nijar Ta Janye Daga Shari'ar Kudaden Da Aka Sace A Mama'aikatar Tsaron Kasa

Shugaba Bazoum

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta kara jaddada aniyar ci gaba da bibiyar shari’ar nan ta mutanen da ake zargi da handame kudaden makamai a ma’aikatar tsaron kasar bayan bayyanar wasu takardun dake nunin hukumomin Nijar sun janye daga wannan shari’a.

Hukumomin sun janye ne daga wanan shari’a saboda ta yi nasarar tatso kudaden da aka wawure daga hannun‘yan kasuwar da abin ya shafasai dai wasu ‘yan fafitika na cewa ba zasu yarda ba da abinda suka kira rufa rufa.

Omar Ibrahim wani daga cikin lauyoyin gwamnatin Nijara ma’aikatar AJE ya na cewa rahoton wucin gadi na binciken wannan badakala da aka fitar a watan Fabrairu 2020 ya yi nunin an cusa billion 48 na cfa a odar wasu kayayyaki ba akan ka’ida ba sai wasu billion 28 na cfa na kayan da aka yi oda amma kuma ba a ba an gansu ba a wani lokacin da wa’adin yin hakan ya shude.

Sai dai kuma an yi katari wannan rahoton wucin gadi ya bayyana a fili ta bayan fage a wani lokacin da ba a ji ba ta bakin mutane da kamfanonin da ake zargi a wannan harka ba lamarin da ya haddasa rudani a kawunan wasu har suke ganin an yi rubda ciki akan billion 76 na cfa a ma’aikatar tsaron kasa.

Daga bisani mutanen da ake zargi sun gabatar da wasu takardunda suka sa aka gano yawan kudaden bai kai inda ake hasashe ba saboda haka yawan kudaden kayan da aka yi oda kuma ba agansu ba sun ja baya zuwa billion 23 na cfa.

Sannan kuma a dai dai wannan lokaci odar wasu daga cikin kayayyakin nan ta iso yayinda ‘yan kasuwar suka yi alkawalin bada sauran kafin karshen watan Afrilu 2020, sai dai kuma matsalar coronavirus ta janyo rufe iyaka.

Bayan haka nan an fitar da wani rahoton karshe a ranar 3 ga watan Afrilu 2020 wanda ya yi nunin daga cikin billion 28 da aka gano a can farko suka koma billion 23 an karbi kayayyaki ko kuma an yi takardun alkawalin shigo da kayan da darajarsu ta haura billion 19 kafin ranar 30 ga watan Afrilun 2020. Sauran kayan billion 4 wasu kamfanonin ketare ne aka ba kwangilarsu.

Sannan kuma a fannin cusen kudaden da aka yi bayan tattara wasu bayanai masu bincike sun sassauta yawan kudaden daga billion 48 da aka bayyana a rahoron wucin gadi zuwa billion 16 da ‘yan kai, kuma tun a watan Afrilun 2020 an gabatar da wannan rahoto a ofishin alkalin alkalai wanda ya damka su ga hukumar ‘yan sandan farin kaya domin ta ci gaba da bincike wanda a karshe aka gano cewa billion 12 da ‘yan kai ne abin ya shafa.

To sai dai shugaban kungiyar Tournons la Page Maikol Zodi dake daya daga cikin masu gwagwarmayar ganin an yi haske a wannan badakala yace ba zasu yarda da abinda ya kira rufa-rufa ba.

Omar Ibrahim a ci gaban bayanansa ya jaddada cewa matsayin gwamnatin ta Nijar bayan ‘yan kasuwar sun biya kudaden da suka ci ba ya nufin karshen zance kenan, shari’ar masu hannu a wannan al’amari da ya jefa jama’ar kasacikin damuwa yanzu aka fara inji shi.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Nijar Ta Janye Daga Shari'ar Kudaden Da Aka Sace A Mama'aikatar Tsaron Kasa