Gwamnatin jihar Neja ta ce ta soke sayarda kujerun aikin hajjin bana da ma'aikatar alhazan jihar ta keyi.
Gwamnatin tace ta gano irin tabargaza tare da cuwacuwar da ma'aikaan suka tafka a lokacin sayarda kujerun aikin hajjin.
A taron majalisar zartaswar jihar gwamnatin ta dauki matakin dakatar da sayar da kujerun.
Mr. Jonathan Vatsa kwamishanan yada labarai ya bayyana dalin da ya sa gwamnatin ta dauki matakin. Yace an tafka cin hanci da magudin wajen bayar da takardun sayen kujerun. Yace takardar da ya kamata a bayar kyauta sai mutum ya biya nera dubu dari biyu, ko fiye da haka, kafin a bashi. Wato ma'aikatan hukumar alhazai suna sayarda takardar ke nan wa jama'a. Takardun kyauta ne kuma na daukan bayanai ne domin alhazan zasu biya kudaden tafiya
Ban da haka an ga takardun a Kano da Kaduna inda za'a sayar dasu. Yanzu gwamnati ta kafa kwamiti. Duk wadanda ya karbi takardar bisa ka'ida za'a bashi sabuwa ya sake cikawa. Wadanda kuma suka yi cuwacuwa su yi kuka da kansu.
Da dama daga cikin al'ummar jihar sun yi marhaban da matakin da gwamnatin jihar ta dauka musamman ganin yadda aka dade ana zargin ma'aikatar alhazan da yin cuwacuwa a lokacin sayar da kujerun zuwa hajji.
Alhaji Mustapha Olsuto yace sautari wadanda ya kamata a basu kujeru basu ake ba ba. Sai kawai a rabawa mutane su je su sayar. Sun mai dashi tamkar wani kasuwanci. Soke sayarda takardun zai taimaka domin wadanda suka dace zasu samu.
Sakataren ma'aikatar alhazan Shaikh Musa Ibrahim yace dawowarsa ke nan daga Saudiya kuma an sanar dashi cewa an canza masa wurin aiki. Amma yace matsalar daga kananan hukumomi ne inda suka tura takardun domin a ba wadanda ke bukatar sayen kujerun zuwa hajji.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5