Gwamnatin Najeriya Zata Gina Tashar Wutar Lantarki A Jihar Imo

FILE - Locals walk past electricity pylons during frequent power outages from South African utility Eskom, caused by its aging coal-fired plants, in Soweto, South Africa, July 3, 2022.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da gina tashar wutar lantarki mai karfin megawatt goma a kogunan Otamiri da kuma Nworie da ke Owerri, babban birnin jihar Imo.

ENUGU, NIGERIA - Gwamnatin jihar Imo ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter ranar Talata, inda ta ce za a gina tashar ne domin samar wa al’ummar Owerri da kewaye isasshiyar wutar lantarki.

Ko da yake, gwamnatin jihar bata ambaci ko naira nawa aikin zai lakume ba, wasu manazarta irinsu marubuci, Dakta Amanze Obi, sun bayyana shakku game da yiwuwar aikin.

“Ina ganin abin yabawa ne. Amma ina fata dai ba siyasa suke yi ba, saboda sai a karshen mulkin Buhari ake neman bijiro da wani muhimmin aiki a kudu maso gabas, a cewar Obi. Ya kara da cewa, ni dai ina da shakku, kuma ina mamakin yadda za a kammala aikin daga yanzu zuwa lokacin da Buhari zai bar mulki.”

Hakazalika, shi ma Chief Osita Nwosu na ganin siyasa ce kawai gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Imo ke yi.

“Kwana nawa ya rage musu a kan mulki? Shin sun tsara komai ko dai maganar baka ce kawai. Ni a ganina siyasa ce kawai,” inji Chief Nwosu.

Sai dai Mista Ifeanyi Nwanguma na ganin yiwuwar aikin, ganin cewa ruwa na gudana sosai a wuraren biyu.

Saurari cikakken rahoton Alphonsus Okoroigwe:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Najeriya Zata Gina Tashar Wutar Lantarki A Jihar Imo