Gwamnatin Najeriya Ta Hanzarta Magance Matsalar Fulani Da Manoma

Shanun Fulani.

Gwamnan jihar Ondo Olusegun Mimiko, yayi kira ga gwamnatin Najeriya ta hanzarta magance matsalar dake tashi tsakanin Fulani da Manoma a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, kafin lamarin ya wuce gona da iri.

Olusegun Mimiko yayi jawabi ne alokacin da ya karbi bakuncin babban Sifeto na ‘Yan Sandan Najeriya, a karshen mako a birnin Okure, inda ya koka game da fadace fadace da ke wakana tsakanin makiyaya Fulani da kuma Manoma Yarabawa.

Wannan kuka na gwamnan Ondo, yazo ne a dai dai lokacin da Fulani ke kokawa game da kashe kashe na dabbobinsu da suke zargin anayi a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya. abinda sukace yana haddasar musu asarar rayukan dabbobi wani lokacin ma harda na al’umma.

Sarkin Fulani Wara na jihar Ogun, yace sunyi ta kai kukansu kan wadannan matsaloli hukumomin suka kamata, amma babu wanda ya dauki mataki. Hakan yasa basu san yadda zasuyi ba.

A cewar Kwamarad Ya’u Musa Sakaba, wakilin wata kungiyar kare hakkin ‘yan Arewa a yankin Yammacin Najeriya, ya tabbatar wa da Muryar Amurka abinda ya kira tauye hakkin Fulani da dabbobin su da akeyi a wannan yanki.

Rikici dai tsakanin Manoma da Makiyaya a Najeriya, za a iya cewa ba sabon abu bane, abune da ya zama ruwan dare gama Duniya, abinda kuma a ko yaushe ake kira ga hukumomi da su tashi tsaye wajen magance wannan lamari kafin ya baci.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamantin Najeriya Ta Hanzarta Magance Matsalar Fulani Da Manoma - 2'20"