Gwamnatin Najeriya ta hana Jami'oin kasar gudanar da Jarabawan tantance dalibai

A jiya talata ne aka gudanar da wani taro akan harkokin ilimi a Najeriya wanda ministan ilimin kasar ya bada wata sanarwa wadda dalibai da dama ke farin ciki da ita.

Ministan ilimi na Najeriya ya fitar da sanarwar soke jarabawar tantance shiga jami’a da aka fi sani da suna post UTME manyan jami’oi ke yiwa dalibai kafin su basu izinin karatu a jami’a bayan jarawar JAMB, a yayin da yake hallartar taron gudanar da tsare tsare na hukumar JAMB a birnin Abuja.

Ministan ya ce jami’oi na iya tantance dalibai da kansu bayan hukumar jam ta basu sakamakon jarabawa, ya kuma kara da cewa jami’oi su guji ba dalibai wata Jarawa bayan wadda aka sani wato JAMB kafin su dauke su .

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta yarda kuma ta amince da ingancin jarabawar da hukumar JAMB ke wa daliban dan haka sakamakon ta kadai ya isa ba sai jami’oi sun sake basu wata jarabawa ba.

An kaiyyade maki dari da tamanin a matsayin wanda dalibi ya kamata ya samu domin can cantar shiga jami’a, kuma babu jami’ar da zata amince da kasa da haka.

Ga rahoton Babangida Jibrin Daga Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Najeriya ta hana Jami'oin kasar gudanar da Jarabawan tantance dalibai 3 '43"