DOMIN IYALI: Mu Muka Mikawa Gwamnati Ya’yanmu
Iyaye Ne Suka Tsaida Shawarar Maida Yammatan Chibok Hannun Gwamnati inji sakataren kungiyar.
Kungiyar iyayen daliban sakandaren Chibok da Boko Haram ta sace, tace sune suka tsaida shawarar maida ikon kula da daliban makarantar dake karatu a Amurka karkashin gwamnatin tarayya.
A cikin hirarsu da Muryar Amurka, sakataren kungiyar Lawal Zanna ya bayyana cewa, iyayen sun kawo masu korafin cewa, rahotannin da suke samu daga ‘ya’yansu na tada masu da hankali, sabili da haka suka nemi shawarar matakin da ya kamata a dauka domin ganin cewa an kyautatawa rayuwarsu.
Bisa ga cewarsu, ‘ya’yan basu gamsu da yanayin da suke ciki ba, yayinda suke korafi a kan tsarin ilimantarwa da sake masu makaranta da aka yi.
Mallam Zana yace wata cibiya mai zaman kanta Murtala Foundation ta basu shawarar gabatar da wannan korafin ga gwamnati da kuma neman gwamnati ta karbi nawayar kula da daliban daga hannun kungiyar dake da alhakin kaisu karatu Amurka.
Ga hirar da Grace Alheri Abdu tayi da Lawal Zanna a shirin Domin Iyali