Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aisha Buhari Ta Dauki Nauyin Jinyar Yaron da Kishiyar Uwarsa Ta Raunata


Yaron mai suna Musa ya fada cikin wannan bala'in ne a hannun kishiyar uwarsa wadda ta tsaga masa harshe, ta karye kafafusan biyu tare da fasa masa ido daya lamarin da yanzu ya sa kishiyar da mijinta duk sun shiga hannun 'yansanda kuma zasu fuskanci shari'a

Bayan da yaron ya fuskanci wannan bala'i a hannun kishiyar uwarsa hukumar hisba ta Kano tare da 'yansanda suka mika yaron wa likitoci a asibitin Murtala dake Kano.

Kakakin rundunar 'yansandan Kano DSP Magaji Musa wanda ya karyata jita-jitan cewa yaron ya rasu yace yanzu ma mahaifin yaron na cikin jerin wadanda ake tuhuma da hannu game da wannan muguwar aika-aikar.

Kawo yanzu dai 'yansanda sun gurfanar da kishiyar uwarsa Zainabu tare da kakarsa gaban kuliya.

To yanzu dai matar shugaban kasar Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta bada umurnin a mika yaron birnin tarayya, Abuja, domin ta dauki nauyin kula da lafiyarsa har ya warke.

Lamarin ya zaburar da hukumar hisbar Kano wajen shirya wa mata wani gangamin fadakar dasu akan amanar kula da yara. Malama Zara Umar mataimakiyar kwamandan hukumar mai kula da bangaren mata tace addinin musulinci ya riga ya tanadi abun da yakamata a yi da yaro idan aure ya mutu to saidai wasu mazan basa bin shirin haka kuma wasu kishiyoyi basu da imani ko tsoron Allah.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG