Alokacin da ministan kudin ta bayyana gaba wani kwamitin Majalisar Dattawa, tace an gano wannan cuwa-cuwar ma’aikatan bogi Dubu 23 ne, ta hanyar amfani da rajistar Banki na VBN da aka samu sunayen wasu jami’ai daban daban a jerin sunayen da ke karbar albashin ma’aikata barkatai.
Ministan kudin tace hatta Bankunan da aka hada baki da su ana wannan cuwa-cuwa to su tabbaci hakika zasu dandana kudarsu.
Majalisar tace a tabbatar an kwato dukkannin kudaden da aka wawure ta wannan hanya, Sanata Shehu Sani, yace, “Wanan aikin ta’asa da ake ta tonowa, a ringa sa mutane sunaye na bogi a matsayin ma’aikatu, wadanda suka wadannan sunayen sune ke amsar albashin wadannan mutane….”
Kwararre kan tattalin arzikin kasa Turakin Tikau, Alhaji Aliyu Sale Bagare, yace tun fil’azal dama cin hanci da rashawa shine babban matsalar Najeriya.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5