Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dawo Da Hajiya Hauwa Mahaifiyar Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba


Jami'an 'yan sanda.
Jami'an 'yan sanda.

Rahotanni daga jihar Taraba Arewa maso Gabashin Najeriya, na cewa awa 74 bayan sace mahaifiyar mataimakin gwamnan jihar Haruna Manu da wasu yan bindiga suka yi a garin Mutum Biyu, yanzu haka ta samu kubuta daga hannun wadanda ke garkuwa da ita.

Kamar yadda mazauna garin Mutum Biyu suka bayyana mahaifiyar mataimakin gwamnan Hajiya Hauwa, yanzu haka tana cikin koshi lafiya. Sun dai bayyana cewa an dawo da ita ne cikin dare da missalin karfe biyu. Amma babu masaniyar ko su waye suka sace ta, kuma ko an biya kudin fansa ko ba a biya ba.

Da yake karin haske daya daga cikin ‘ya ‘yan ta Hassan Manu, ya bayyana jin dadin sa ga dawo da mahaifiyarsa da akayi, amma yace ba a biya komai ga wanda suka yi garkuwa da ita.

To sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Tarabar na fa tutitayar cewa sune suka ceto mahaifiyar mataimakin gwamnan jihar. Kwamishinan yan sandan jihar CP Alkali ya bayyana cewa basu zauna ba tun da suka sami labarin an sace ta, da taimakon Allah yanzu an dawo da ita.

A cikin kwanakin nan dai ana samun karuwar matsalar satar mutane ana garkuwa da su domin neman kudin fansa.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG