Gwamnatin Najeriya Ta Kulla Yarjejeniya Da Tsagerun Niger Delta

Wani Bututun Mai Da Aka Fasa

Gwamnatin Najeriya ta cimma shirin tsagaita wuta da tsagerun Niger Delta da ke kai hare-hare akan bututan man man kasar, a cewar wani babban jami’in kamfanin matatar man kasar a hirar da ya yi da Muryar Amurka a yau Talata.

Sai dai mayakan kungiyar Niger Delta Avengers ta musanta cimma wata matsaya da gwamnati, inda ta rubuta a shafinta na Twitter cewa, zancen ba shi da tushe ballantana makama.

Kungiyar dai ta sha daukan alhakin kai hare-hare akan bututan man kasar, lamarin da ya kassara yawan man da kasar ke fitarwa mai yawan ganga miliyan biyu a kowace rana.

Masana tattalin arziki sun alakanta matsalar tabarbarewar tattalin arzikin da Najeriyar ke fuskanta da aika-aikan da tsegerun na Niger Delta ke yi.

Najeriya ita ce kasar da ta fi kowace samar da man fetur a nahiyar Afrika.

Labarin cimma matsayar tsagaita wutar, ya samo asali ne tun bayan da ministan man fetur din kasar Ibe Kachikwu ya kai ziyara yankin na Niger Delta.