Fadar gwamnatin Najeriya ta Aso Rock ta bukaci 'yan adawa da ba su yi nasara ba a kararrakin zabe ba da su jira hukuncin kotun koli, maimakon su rika zargin cewa ana yi mu su kafar angulu.
Wannan ya biyo ne bayan zanga-zangar da magoya bayan wasu gwamnonin adawa su ka yi, inda su ka bayyana zullumin da su ke da shi kan rashin tabbas game da samun nasara a kotun koli.
'Yan adawar dai sun yi zanga-zangar ne a jihohin Kano da Nasarawa inda su ka nemi sai lallai a bi mu su kadi a shari'ar da su ke cewa sun lashe zabe ta hanyar da ba tantama a cikin ta.
Mai ba shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan al’amurran siyasa, Ibrahim Kabir Masari ya ce ba wani dalilin da zai sa shugaban kasar ya yi katsalandan ga lamuran shari'a, wanda bangare ne mai cin gashin kan shi.
Masari ya kara da cewa, gaggawa na damun wasu masu hamaiya da kan yi riga Malam masallaci a batun da ya shafi yanke hukunci, wanda lamari ne da ya shafi shari’a.
Gwamnonin adawa irin na jihohin Kano, Zamfara, Filato da sauarn su, tuni suka shigar da kararraki a gaban kotun koli sakamakon rashin nasara a kotunan daukaka kara.
Kwamishinan watsa labarai na jihar Zamfara ya ce ba kamar yanda kotun koli ta kwace daukacin kujerun APC a jihar ba a shekarar 2019, a wannan karon su na da yakinin lashe zabe.
Su kuwa jigajigan jam'iyyar NNPP, wadda ita ce jam’iyar da ta lashe zaben jihar Kano, nunawa su ke yi cewa, ana yiwa tafiyar Rabiu Musa Kwankwaso makarkashiya, duk da dai sun ce hakan ba zai karya mu su guiwa ba.
Wani babban jigon jam’iyar NNPP Buba Galadima ya sha bayyana Alhaji Rabi’u Musa Kwankwason a matsayin madugu uban tafiya a harkar siyasa.
Yanzu dai baki daya kallo ya koma sama, inda ake jiran aji yadda za ta kaya a hukuncin da kotun koli za ta zartas.