Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Najeriya Ta Kirkiro Ma'aikatan Kula Da Tattalin Arzikin Teku Domin Samun Kudaden Shiga


Bola Tinubu
Bola Tinubu

Gwamantin Najeriya tasha alwashin cigaba da nemo wasu hanyoyin samun kudaden shiga domin bunkasa tattalin arzikin kasar, maimakon dogaro da man fetur.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana hakan a wajen taron kasa na hukumar kwastan a birnin lagos.

Shugaba Bola Tinubu na Najeriya wanda mataimakin sa, Sanata Kashim Shettima ya wakilta, yace kamar yarda yayi alkawari fatan gwamnatin sa shine bunkasa wasu fannonin samun kudaden shiga da zasu taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya, a maimakon dogaro da man fetur.

Wannan nema yasa gwamnati ta kirkiro ma'aikatan kula da tattalin arzikin Teku domin samun kudaden shiga inji shugaban.

Shugaba Tinubu wanda ya yaba da kokarin da hukumar kwastan keyi na tara kudaden shiga da kuma saka ido akan iyakokin kasar yace gwamnati zataci gaba da bada goyon bayanta ta wannan fuska.

A bangaren sa babban konturolan kwastan na kasa Bashir Adewale yace shekaru 12 kenan rabon da a gudanar da taron hukumar na kasa,taron kuma da aka shirya domin karawa jami'an na kwastan kwarin guiwa da fadakar da jama'a game da aiyukan hukumar.

Yasha alwashin hukumar zata ci gaba da tafiya da zamani wajen samun kididdigan kayayyakin da ake shigowa dasu cikin kasa domin bunkasa kudaden shiga.

Don haka yayi kira ga jama'a musanman 'yan kasuwa dake shigowa ko fita da kaya ciki da wajen Najeriya su kasance masu bada hadin kai wajen ciyar da kasar gaba.

A bangaren sa gwamnan jihar lagos Babajide Sanwolu yabawa yayi da gudumawar hukumar kwastan wajen bunkasa tattalin aezikin jihar lagos dama kasa baki daya. Yana mai cewa gwamnati da kuma al'umar jihar zasuci gaba da taimakaw hukumar domin bunkasa tattalin arzikin kasa baki daya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG