A taron da ma’aikatar ta kammala a Inugu, babban birnin jihar Inugu jiya Laraba, babban jami’in sashen kula da marasa aiki masu dawowa daga kasashen ketare Dakta Sunday Onazi ya ce an shirya taron ne don inganta iyawar jami’an kwadago a ofisoshi na yankin kudu maso gabas kan yadda za a tafiyar da harkokin cibiyoyin sana’a da ke fadin yankin.
Dakta Onazi ya kara da cewa, “alhaki ya rataya ne akan gwamnatin tarayya ta kirkiro kyakkyawan yanayi na samar da aikin yi, kuma saboda haka ne ma’aikatar ta kafa cibiyoyin sana’a 24 a fadin yankuna shidda na Najeriya. Kuma akwai bukatar horas da jami’an da zasu rika aiki a wadannan cibiyoyin sana’a.”
A nata bayanin kwanturolar ofishin kwadago na jihar Imo Malama Winifred Nkwota, wacce ta halarci horaswar ta bayyana cewa, zasu koma su horas da masu horaswa, don cibiyar sana’ar a jihar ta cimma ainihin muradun da suka sa aka kafa ta. Kuma sun karu sosai da wannan horaswar saboda yanzu sun san yadda ake shawartar wadanda suka dawo daga kasashen waje da ke neman aikin yi.
Sashen tattalin arziki da harkokin zamantakewa na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce adadin ‘yan Najeriya da suka fice daga kasarsu don neman ingantuwar rayuwa a shekarar 2020 ya kai miliyan daya da digo bakwai, kuma don irin masu dawowa daga cikin wadannan mutanen ne ma’aikatar kwadago ta Najeriya, ta ce aka kafa cibiyoyin sana’a a fadin kasar.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna