Gwamnatin tarayya ta biya ragowar bashin da kamfanin sufurin jiragen sama na tarayyar Turai ke bin ta da yakai har dala miliyan 850.
Jakadiyar Tarayyar Turai a Najeriya da Kungiyar Raya Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), Samuela Isopi, ce ta bayyana hakan a yayin taron bunkasa kasuwanci tsakanin Najeriya da kungiyar kasashen Turai (EU) karo na 9 da ya gudana a Abuja a yau Talata.
Isopi ta kara da cewa, har yanzu Najeriya ce kan gaba cikin kawayen kasuwancin EU a shekarar data gabata inda take da alakar cinikayyar da ta kai kimanin Euro biliyan 35.
Ta kuma ce, Najeriya ce babbar mai zuba jari a kasuwar Tarayyar Turai inda take da hannayen jarin da aka kiyasta zasu kai Euro bilyan 26, kwatancin kaso 1 bisa 3 na jarin Najeriya dake ketare.
Isopi ta cigaba da cewa, akwai fiye da kamfanin tarayyar Turai 230 dake aiki a Najeriya, inda suke samar da guraben aikin yi ga matasa da mata.