WASHINGTON DC - Gwamnatin tarayyar Najeriya tace tana duba yiyuwar sakewa kurkukun dake garin Suleja na jihar Neja matsuguni, sakamakon tserewar da fursunoni 119 suka yi.
A yayin ziyarar daya kai kurkukun a yau Alhamis, Ministan Harkokin Cikin Gida na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewar kurkukun na dauke ne da fursunoni 499, sabanin 250 da aka kiyasta zai iya dauka tunda fari.
Ya kuma tabbatar da tserewar fursunoni 119, saidai ya kara da cewar; an yi nasarar sake kama 13 daga cikinsu.
Bayanin nasa ya biyo bayan rahotannin dake cewar hukumomin kurkukun zasu wallafa sunaye da hotunan fursunonin da suka arce daga gidan yarin.
In ba a manta ba Muryar Amurka ta bada rahoton arcewar fursunoni 118 daga kurkukun sakamakon samun mamakon ruwan sama.
Mamakon ruwan saman da aka shatata da ya haddasa mummunar barna ga kurkukun mai matsakaicin tsaro dake garin Suleja na jihar Neja, abinda yayi matukar lalata gininsa.
Ruwan saman yayi matukar lalata ginin kurkukun, ciki harda rusa katangar data kewaye shi, abinda ya baiwa wasu fursunoni damar arcewa.