Babban daraktan hukumar kiwon lafiya matakin farko ta kasa (NPHCDA) Faisal Shu’aib ne ya bayyana haka, a wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin hukumar na Abuja.
Daraktan yace gwamnati za ta iya amfani da tsarin doka kan mutanen saboda kin amincewa da yin rigakafin, wanda hakan zai iya jefa wasu mutane cikin hatsari.
Ya kara da cewa idan mutanen na da ‘yancin kin yin allurar rigakafi, to amma kuma basu da ‘yancin cutarwa ko kuma barazana ga lafiyar wadansu.
Har yanzu dai tsarin karbar allurar rigakafin cutar korona, babu mata masu juna biyu da kananan yara.
Idan za’a iya tunawa a makon da ya gabata ne gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya umurci ‘yan jihar da su yi allurar rigakafin, yana mai cewa daga ranar 15 ga watan Satumba, duk wanda bai yi rigakafin ba za’a haramta masa shiga wuraren taruwar jama’a kamar bankuna da wuraren Ibada.
To sai dai kuma wata kotu a jihar ta ba da umarnin dagatar da daukar wannan matakin na wani lokaci, biyo bayan kara da aka shigar a gabanta kan lamarin.