Sun yi hakan ne don tabbatar da cewa an aiwatar da tsare-tsaren ci gaba mai dorewa a matakai daban-daban na tattalin arziki a kasar.
Jiga-jigai daga ma’aikatun gwamnatin Najeriya tare da na Majalisar Dinkin Duniya ne suka sanya hannu a kan tsarin hadin gwiwar na shekarar 2023 zuwa 2027 a cikin ginin MDD dake birnin tarayya Abuja inda suka ce tsarin zai maida hankali ne a kan taimakawa Najeriya don cimma manufofin ci gaba mai dorewa, tabbatar da hadin kai, da gudanar da ayyukan gwamnati a bayyane.
A yayin rattaba hannu kan takardar sabon tsarin a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Abuja, babban jami’in majalisar a Najeriya, Matthias Schmale, ya ce sun sabunta alkawuran da suka dauka na yin aiki tare a cikin shekaru biyar masu zuwa.
Alkawuran dai sun kunshi ci gaba da gano manyan kalubalen da Najeriya ke fuskanta kamar yawan matasa da basu da aikin yi, yawan yara da ba sa zuwa makaranta da kuma yawan mutanen da ke fama da talauci a kasar.
A cewar karamin ministan kudi da tsare tsare, Clem Ikanade Agba, tsarin da suka sanya hannu a kai zai kara taimakawa wajen cimma nasarar a alkawarin da gwamnatin tarayyar kasar ta yi na fitar da karin ‘yan Najeriya miliyan 35 daga kangin talauci nan da shekara ta 2025 ya na mai cewa ya zama wajibi gwamntocin jihohi su mayar da hankali kan yaki da talauci a yankunan karkara a maimakon sanya ido a kan birane kawai.
A nata bangare, shugabar tawagar gudanarwar tsarin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Najeriya da Majalisar Dinkin Duniya, Ms Ulla Mueller, ta bayyana cewa tsarin nasu zai taimaka matuka gaya ga Najeriya da tsarin ci gaban kasar tare da mayar da hankali a kan muhimman batuttuwa da suka hada da daidaiton jinsi na bai daya, karfafawa mata su rika samun damar tsarin lafiyar haihuwa da yadda za a shigar da su cikin harkokin ci gaban tattalin arziki.
Ministar ayyukan mata, Pauline tallen, ta ce wannan tsarin da aka rattabawa hannu na da kyau saidai batun aiwatarwa shi ne damuwa inda ta yi kira a kan cewa a sami matattakalar da za’a tabbatar da bada mahimmanci ga abubuwan da suka shaki mata da matasa.
Majalisar Dinkin Duniya da takwarorinta a Najeriya na aiki tukuru don cimma kudurorin nan na ci gaba mai dorewa mai manufofi 17 masu alaka da juna wadanda ke magance manyan kalubalen ci gaban da mutane ke fuskanta a Najeriya da ma duniya baki daya.
Tun lokacin da aka amince da manufofin ci gaba mai dorewa na SDGs a watan Satumbar shekarar 2015 ne Najeriya ke ci gaba da bayyana aniyar ta na cimma kudurorin na duniya ta hanyar jagoranci da mallakar tsarin aiwatarwa.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5