A zaman kotun na ranar Juma’a a karkashin jagorancin mai shari’a M.A Udumeh, alkalan kotun guda uku sun amince da hukuncin kotun baya kan cewa, daga cikin adadin kuri’un da aka jefa wa gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, fiye da kuri’u dubu 165 na bogi ne.
Baya ga haka, kotun ta amince da da’awar jam’iyyar APC mai cewa gwamna Abba Kabir ba dan jam’iyyar NNPP ba ne, a saboda haka ba shi da hurumin tsayawa takara a karkashin inuwar jam’iyyar.
Yanzu haka dai wasu ‘yan jihar Kano, musamman magoya bayan jam’iyyun APC da NNPP sun fara tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan hukunci na kotun daukaka kara ta Abuja.
“Alhamdulillahi! dama abin da muka zata kenan, gaskiya tayi halinta," Inji Kabiru Maigoro, wani mai goyon bayan Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC.
Shi kuwa, wani matashi da ke goyon bayan gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya ce sam wannan hukuncin bai yi dadi ba, a ce wai mai girma gwamna Abba ba dan jam’iyya ba ne, "ai ka ga an zo da son zuciya."
Sai dai a cewar Barrister Haruna Isa Dederi, kwamishinan shari’a na jihar Kano, gwamnatinsu da jam’iyyar NNPP zasu kai kara kotun koli.
“Kowane irin hukuncin kotu ya kan zo ne daidai da fahimtar alkali ko alkalan kotun, kuma wadannan alkalai sun yanke hukunci ne bisa fahimtar da suka yi wa lamarin, a don haka ba sai an fada ba, babu shakka za mu tafi kotun koli," a cewar Dederi.
To amma sakataren jam’iyyar APC ta jihar Kano Hon Ibrahim Zakari Sarina, ya ce sun yi maraba da wannan hukunci na kotun daukaka kara, kuma hakan ya tabbatar da da’awa da kuma hujjojin da suka gabatar wa kotu.
Tun a daren Alhamis ne dai aka jibge jami’an tsaro a sassa dabam dabam na birni da kewayen Kano, a wani mataki da hukumomin tsaro suka dauka na tabbatar da doka da oda.
Ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoton, al’uma a sassan birni da kewayen Kano na ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum bisa doka da oda.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5