Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta shigar da daurarru cikin tsarinta na daukar nauyin kiwon lafiya da nufin samar musu da ingantaccen tsarin kiwon lafiya kyauta yayin da suke daure.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da gidajen gyaran hali na Kano, csc Musbahu Kofar-Nasarawa ya fitar, a yau Litinin a Kano.
Kofar-Nasarawa ya ruwaito babbar sakatariya a hukumar kula da kiwon lafiya ta jihar Kano, Dr. Rahila Aliyu-Mukhtar, na bayyana hakan yayin ziyarar data kaiwa shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali na Kano, Controller Ado Salisu, a ofishinsa.
Rahila Aliyu-Mukhtar tace Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da shigar da daurarrun cikin tsarin kiwon lafiyar, domin basu damar cin gajiyar ingantaccen tsarin kiwon lafiya kyauta yayin da su ke tsare.
“Walwalar fursunoni ta bangaren kiwon lafiya nada mahimmancin gaske a bangaren gudanar da gidajen yari yadda ya dace da kuma samun nasarar gyaran halayya da sake tsugunar dasu da sake mayar dasu cikin al’umma,” a cewarta.