Hakan dai na zuwa ne kwanaki uku kafin gudanar da Mukabalar da gwamnatin Kano ta ce za’a yi a ranar Lahadi mai zuwa.
Kungiyar ta Jama’atu Nasaril Islam da ake kira JNI a takaice, mai shalkwata a Kaduna wadda mai alfarma sarkin musulmi ke jagoranta na cikin jerin kungiyoyin da gwamnatin ta nemi su zama ‘yan kallo a wurin mukabalar.
Sai dai a sanarwar da ta fitar ranar Laraba, kungiyar ta JNI ta ce ba za ta halarci taron mukabalar ba wadda aka shirya yi a fadar mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.
A cikin hirar shi da Muryar Amurka, Dr. Khalid Aliyu sakatare janar na kungiyar ta JNI ya ce duk mutumin da ya yi wa annabi abinda wannan bawan Allah ya yi, Allah ba zai bar shi ba.
Dangane da furcin da wasu ke yi cewa wannan mataki na kungiyar JNI ka iya kawo rabuwar kai musamman tsakanin malamai, la’akari da yadda bakin su ya zo daya a farkon lamarin, Dr. Khalid ya ce an sami hadin kai da farin ciki da gwamnati ta dakatar da shi ta kuma rufe masallacinsa, kuma gwamnati ta shammacesu ne saboda harkar ta malamai ce tun da batu ne na addini.
Tuni dai wasu daga cikin al’uma ke ganin wannan matsaya ta kungiyar JNI ta zo a makare saboda kwanaki kalilan suka rage a yi wannan mukabala.
Dr, Khalid ya ce, gwammati ta makara wajen dakile fitina da kwata-kwata a kasa dakile ta.
To amma gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani ga kungiyar ta JNI da ma wasu malamai masu ra’ayi irin nata.
Da ya ke tsokaci dangane da lamarin, Comrade Mohammed Garba, kwamishinan labarun gwamnati ya ce Abduljabar ne ya nemi a yi wannan mukabala, daga nan malamai suka ce sun yarda da bukatarsa suka kuma rubuta wasikar amincewa zuwa ga gwamnati. Ita kuma gwamnati ta ce za ta tabbatar da bada cikakken tsaro da wuri da ya dace.
Yanzu lokacin zai tabbatar da wakanar wannan mukabala ko akasin haka.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: Abdul Jabbar Nasiru Kabara, Alhaji Aminu Ado Bayero, jihar Kano, JNI, Nigeria, da Najeriya.