Gwamnatin Kaduna Tayi Bayanin Dalilin Dokar Hana Fita Dare da Rana

Trwatsewar bamabamai a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna tayi bayanin dalin kafa dokar hana fita dare da rana a wasu kananan hukumomin jihar biyo bayan tashin bamabamai biyu a birnin Kaduna.

Daraktan yada labaru na gwamnan jihar Kaduna Alhaji Ahmed Abdullahi Maiyaki wanda ya sanar da kafa dokar yace gwamnati na so ne ta ba jami'an tsaro damar gudanar da aikinsu game da fashewar bamabamai guda biyu a garin Kaduna.

Yace dokar ta zama wajibi domin gwamnati da jami'an tsaro su samu su gudanar da bincike da wasu ayyuka na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama'a musamman cikin babban birnin jihar Kaduna sabili da abun takaici da ya faru.

Dokar ta shafi cikin garin Kaduna da kananan hukumomin Kaduna ta Kudu da Kaduna ta Arewa da Rigachukun. Dokar ta fara aiki nan take na sa'o'i ashirin da hudu , wato ba dare ba rana har a ga abun da hali yayi.

Tagwayen bamabaman sun tashi ne a titin Alkali da Kawo. Na titin Alkali ya tashi ne jim kadan bayan rufe tafsirin Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Bam na biyu ya tashi ne a Kawo daf da motar tsohon shugaban kasa Janaral Muhammed Buhari kimanin sa'o'i biyu da tashin na farko.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Kaduna Ta Bayyana Dalilin Dokar Hana Fita Dare da Rana - 6' 02"