Babban sakataren kungiyar IZALA na kasa Sheikh Muhammed Haruna Gombe yayi tur da tashin bamabamai a garin Kaduna yayin da yake rufe tasfirin Kur'ani mai girma na watan azumin Ramadan na wannan shekarar a Sokoto.
Kungiyar tana ganin rashin tsaro ya kai halin lahaula a Najeriya abin da tace ya zama wajibi ga mahukuntar kasar da su dauki kwararan matakan shawo kan matsalar. Sheikh Haruna Gombe yace shin masu daukan bamabaman wadanne hanyoyi suke bi har da ba'a ganinsu. Idan hanyoyin da mutane ke bi suke anfani dasu to babu inda babu jami'an tsaro masu binciken kowa. Idan hanyoyin suke bi to shin yaya aka yi suna wucewa da bamabamai ba'a samu an kamasu ba. Akwai abun dubawa a lamarin. Wajibi ne gwamnati ta ji tsoron Allah.
Komawa ga Ubangiji da dagewa da yin addu'o'i na daga cikin shawarwarin da kungiyar Izala ta baiwa al'ummar Musulmai da ma 'yan Najeriya baki daya.
Shehun malamin yayi addu'ar Allah ya tona masu aikata ta'adanci. Idan karfi garesu Allah ya ruguzar da karfin. Idan kuma iko ne garesu Allah ya karbe ikon.
Daga bisani Sheikh Haruna Gombe ya jaddada bukatar neman ilimi da sana'o'i a tsakanin matasan Najeriya. Ya kira matasa su tsaya su yi karatu idan kuma suka ki bayi zasu zama. Yace idan aka maida matasa 'yan bangan siyasa ana basu kwaya suna sha ba'a yi masu adalci ba. Yace su duba duk wadanda ke 'yan bangan siyasa babu wani dan gwamna ko dan attajiri ko dan dan majalisa. 'Ya'yan talakawa ake yin anfani dasu.
Akan zaben shekara mai zuwa ya kira matasa da suyi karatun ta natsu su kuma tabbatar da cewa sun zabi shugabanni na gari domin a samu zaman lafiya kasar kuma ta samu ta cigaba. Yace lokacin siyasar kudi da bada babur da tufafi duk ta wuce. A zabi shugabannin kwarai domin babu abun da za'a iya canzashi sai da shugabanci nagari.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna