Janaral Muhammed Buhari ya fito daga Kaduna zai tafi Daura lamarin ya faru kamar yadda shi kansa ya fada.
Yace sun kama hanya ne sai wadanda suke da bam a motarsu suka so su wucesu amma motar da take biye dashi sai ta hanasu. Da suka kai Kawo sabili da kasuwa da cunkoson mutane babu yadda motar 'yansanda dake yi masa jagoranci a gaba zata iya gudu. A cikin wannan yanayin ne masu dauke da bam din suka tarwasashi.
Bam din yayi sanadiyar lalacewar motocinsa guda uku. Shi ya fito babu abun da ya sameshi amma koda ya fito ya ga mutane a zube, wato wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka jikata. Cikin wadanda suka jikata har da nashi mutanen uku. Yace an kaisu asibiti an yi masu magani an sallamesu.
Motar dake gabansa ta 'yansandan dake tare dashi ne. Motar kuma dake bayansa ta sojojin dake aiki dashi ne tare da wasu jami'an tsaro a fararen kaya amma suna dauke da makamai.
Kafin aukuwar wannan lamarin Janaral Buhari yace babu wata barazana ga rayuwarsa domin babu wanda ya taba rubuto masa ko ya furta wani abu mai kaman hakan. Dalili ke nan da yace abun ya bashi mamaki.
Ga cikakken bayani.