Gwamnatin jihar Neja ta yi maraba da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na hana sayar da codeine a duk fadin kasar saboda ya zama abun da mutane ke sha ya sasu maye.
Dubban matasa ne ke shan codeine domin ya bugar da su.
Kawo yanzu gwamnatin jihar Neja ta ba da sanarwar rufe shagunan magani har guda 20 da aka samu suna sayar da haramtacen maganin.
Kwamishanan kiwon lafiya na jihar Dr Mustapha Jibril ya yi karin bayani akan abun da suka yi. Yace gwamnan jihar ya sa masu ilimin magani suna bi shago shago kuma duk inda suka ga ana sayar da magani codeine ba tare da mai saye ya bada takardar izini daga hukuma ba sai su rufe shagon.
Bincike ya nuna cewa a jihar Neja matasa maza da mata ke anfani da codeine. Wata da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana irin anfani da take samu daga shan codeine din. Ta kuma ambaci sunayen wasu magungunan da suke sha domin bugar da su baicin codeine.
Shugaban shirin tallafawa matasa na jihar, Alhaji Umar Kolo ya ce suna kokarin fadakar da matasan amma akwai bukatar sanya hannun sauran jama’a kamar su malaman addinai da iyaye domin a dinga lura da irin shagunan da ake dasu a unguwanni.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani