Jaridun Najeriya da dama sun bugo wannan labari dake nuna cewa wadannan gungun matasa har ma sun sami nasarar tsayar da jerin gwanon motocin gwamnan, tare da furta wasu kalamai da suka shafi albashin ma’aikata da kuma wasu kudaden fansho da ake cirewa ma’aikatan.
To amma a wani taron manema labarai a yammacin jiya Talata, kakakin gwamnan Jibril Baba Inda, yace labarin babu kanshin gaskiya a cikin sa. Yace gwamnan na hanyar sa ta zuwa wani taron Polio da akayi, ya tsaya wata hanya yana jiran a basu hannu inda wasu matasa suka je suka gaishe shi, ya kuma zanta da su.
A baya dai gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello, ya fuskanci maganganu da dama daga wasu al’ummar jihar akan yawan tafiye tafiye zuwa kasashen waje, da mahukuntan jihar suka ce yana yi ne domin nemo masu zuba jari a jihar. haka zalika ko a makon jiya ma majalisar dokokin jihar Neja ta nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnan ke binciken kudaden da suka bace a lokacin gwamnatin da ta gabata.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5