A jihar Neja gwamnati ce ta tallafawa iyalan wadanda aka kashe a rikicin da ya barke tsakanin sojoji da mutanen kauyen Kofa a karamar hukumar Boso da kudi Nera miliyan 26.
Tun a watan Augustan shekarar 2016 ne aka samu tashin hankalin a kauyen inda sojoji 12 da fararen hula 16 suka rasa rayukansu.
Taimakon da gwamnati ta bayar ya shafi iyalan sojojin da suka mutu da kuma iyalan fararen hular.
Alhaji Ibrahim Inga shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Nejan ya ce kawo yanzu gwamnatin jihar ta kashe wa iyalan mamatan Nera miliyan 26. Akan kowane mutum da ya mutu an ba iyalansa Nera dubu dari hudu ba a matsayin diya ba, amma a matsayin tausayawa da gwamnan jihar ya yi masu. Ya kara da cewa tallafin sojojin sun turawa hukumar tsaron jihar wadda zata rabawa iyalansu.
Tun aukuwar lamarin gwamnatin jihar ta ce ta nada kwamitin bincike domin gano musabbabin abun da ya haddasa rikicin. Sai dai har yanzu babu wani labari akan rahoton kwamitin.
Alhaji Mamman Musa kwamishanan ruwa na jihar, shine ya wakilci gwamnan jihar a wajen raba tallafin. Yace suna jiran rahoton binciken kuma da zarar ya fito ba za’a boyeshi ba.
Wasu cikin fararen hulan da suka samu tallafin sun bayyana ra’ayinsu. Usman Saidu wanda ya rasa dansa, ya ce lokacin da lamarin ya auku ya sasu juyayi amma kuma dole a hakura. Shi ko Panta ya ce ‘ya’yanshi biyu aka kashe. Akan tallafin da aka basu a cewarsa ya zama abun tausayi dole ne ya karba.
Baya ga tallafin kudin da aka bayar akwai kuma buhun shinkafa da masara da sauran kayayyakin masarufi da aka raba masu.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari
Your browser doesn’t support HTML5