Gwamnatin Jihar Bauci ta ba Nakasassu Tallafi

Wasu nakasassu.

A wani yunkuri na na rage ma nakasassu da masu fama da mawuyacin talauci gwamnatin jihar bauchi ta fito da wani shirin tallafa masu.
Yayin da jihar Bauchi ke fuskantar kwararowar mutane musamman nakasassu daga jihohin dake fama da tashin hankali, gwamnatin jihar ta fito da shirin taimakawa nakasassu 'yan asalin jihar.

An yi taron nakasasu na jihar Bauchi domin tallafa masu da kayan abinci. Alhaji Fijiru Abdu shugaban nakasassu na jihar Bauchi ya gabatar da jawabi a wurin taron inda ya ce taron na zuwa tayasu murna ne da farin ciki. Yace yana son ya kara fadakar da nakasassu kowa ya je ya yi adalci kuma su tsaya da yin addu'a.

Nakasassun sun fasara tallafin da suke samu cewa tallafi ne domin mutum ya daina bara. Kuma hakika bara ta yi sauki a Bauchi. Yace bara ta ragu. Yawancin wadanda suke bara yanzu a Bauchi baki ne wadanda gwamnoninsu basu yi masu adalci ba kamar yadda ake yi masu a jihar Bauchi.

Cikin kayan abincin da aka basu akwai shinkafa da masara da gyero da sukari da dai wasu kayan. Shugaban nakasassun yace komi gwamnan jihar ya basu.

Alhaji Alasan Tata Gurgu sarkin guragun Ningi yace rana ce ta farin ciki ga duk wani nakasasshe dan asalin jihar Bauchi sakamakon tallafi da tausayawa da gwamnan jihar ya nunawa nakasassu. Kan wai tallafin domin su daina yawon gararamba da yin bara a kan hanya ne sarkin yace ba zasu iya hana kowa ya daina bara ba amma ta ragu. Yace wadanda bala'in tashin hankali ya addabesu suka kwararo wurinsu suna bara.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba Nakasassu Tallafi - 2'45"