Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kama Ma'aikata 'Yan Kasashen Waje Su 7 A Jihar Bauci.


Wani yaro yake zaune kan wata motar 'Yansanda da aka kona, a wani hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Kano.
Wani yaro yake zaune kan wata motar 'Yansanda da aka kona, a wani hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Kano.
A jihar Bauci dake arewa maso gabashin Najeriya, 'yan bindiga sun kama ma;aikata 'yan kasashe ketare su bakwai, suka kuma kashe maigadi daya a lokacin wani hari da suka kai kan sansanin kamfanin aikin gine gine na wani kora daga lebanon.

'Yan Sanda suka ce 'yan bindigan sun farwa sansanin kamfanin da ake kira Setraco dake garin jama'are cikin jihar Bauci a daren jiya Asabar, daga bisani suka tsere da ma'aikatan da suka kama.

Hukumomi suka ce ma'aikatan da aka kama sun hada da 'yan kasashen Britaniya, da Italiya, da Girka,, da akalla 'yan Lebanon biyu.

Babu wanda ya fito nan da nan ya dauki alhakin kai harin.

Hukumomin Najeriya da farko 'yan bindigan sun kaiwa wani gidan fursina da da ofishin 'yansanda hari a yankin, amma aka fi karfisnu a duka yunkurin biyu da suka yi.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG