Gwamnatin Jamhuriyar Nijar Ta Kulla Yarjejeniya Da Bankin Musulunci

Jami'an bankin Musulunci da Ministar Fasalin Kasar Nijar

Yanzu haka bankin Musulunci na IDP ya dauki nauyin wasu muhimman ayyukan raya kasa a Jamhuriyar Nijar.

Wata tawagar shuwagabanin bankin Musulunci na IDB mai cibiya a birnin Jiddah da ke kasar Saudi Arebiya, suna gudanar da ziyara a wasu kasashen Afirka Ta Yamma cikin su har da jamhuriyar Nijar.

Mai magana da yawun bankin IDB Mohammed Jamil Yusha'u ya ce, makasudin wannan ziyara ta shugaban bankin IDB ko BID Bandar Al-Hajjar a yankin Afirka Ta Yamma da ake kira Transformers tour, domin kara karfafa huldar aiki a tsakanin bankin da gwamnatocin wadanan kasashe.

Sannan ya kara da cewa, kasashen za su amfana da wani tsarin tallafin da ke mayar da hankali akan wasu muhimman ayyukan ci gaban al’umma.

A karkashin yarjejeniyoyin da suka kulla da hukumomin jamhuriyar Nijar, Bankin na Islamic Developement ya kaddamar da wasu ayyuka na musamman.

Ga dai wakilinmu a Yamai Sule Mummuni Barma da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar Ta Kulla Yarjejeniya Da Bankin Musulunci