Gwamnatin jihar Imo ta fito da wani sabon tsari na binciken kwakwaf akan duk wasu kayan da manyan motoci ke daukowa daga yankin arewacin Najeriya kafin a saukesu a mota domin tabbatar da cewa ba'a dauko wani abu mai kama da bama-bamai ba.
Kayayyakin da ake kawowa daga arewa sun hada da kayan gwari kamar su tumatur da albasa da wake da dai sauransu. Wannan lamarin na cigaba da kawo ccekuce tsakanin 'yan asalin arewacin Najeriya da lamarin ya shafa.
Mai ba gwamnan Imo shawara akan baki Faisal Lawal ya bada bayani. Bisa ga shirin tsaron jihar gwamnan ya kira taro inda ya bayyana cewa kowace irin mota babba mai daukan kaya ana son a binciketa. Yace abun ya shafi kowane irin kaya muddin babbar mota ta dauko kayan. Yace idan dare yayi idan babbar mota ce an hanata shiga garin sai gari ya waye. Tsarin zai taimakawa 'yan kasuwa.
Amma 'yan arewacin Najeriya da lamarin ya shafa sun bayyana ra'ayoyinsu. Alhaji Musa Zakari Yau yace bayanin bai yi masu dadi ba kuma basu yi tunanen gwamnan jihar zai yi wannan irin bayanin ba musamman shirin cewa a kai motocin wani wuri daban, a sauke kayan, a bincikesu, kana a sake mayar da kayan cikin motocin. Wani Babale yace tumatur ba wake bane ko shinkafa. Yace muddin aka sauke tumatur to anan za'a rabu dashi idan ba haka ba kuma ya baci.
'Yan arewa 'yan kasuwa sun roki gwamnan ya sake duba lamarin. Idan so samu ne ya turo masu bincike a idan ake sauke kayan a bincika kafin a sayar da su.
Amma kwamishanan rundunar 'yansandan jihar ta Imo yace akwai wata jita-jita da aka yada cewa an samu bam a wata mota da ta dauko albasa. Yace wannan magana ba gaskiya ba ce. Amma domin a kawar da jita-jita gwamnati ta ga yakamata a daina sauke kaya da daddare sai da safe ido na ganin ido.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.
Your browser doesn’t support HTML5