Hukumomin kasar Sin wato China sun dauki matakan hana yin azumin watan Ramadan ga Musulmi 'yan kabilar Uighur da ke zaune a lardin Xianjing da ke arewa maso yammacin kasar.
Hukumomin na kasar Sin sun haramtawa ma'aikatan gwamnati da daliban makarantu yin azumi, al'amarin da kungiyoyin kare hakkokin Bil Adama suka ce ya zama wata hanyar da gwamnatin Sin ke yin amfani da shi kowace shekara a yunkurin ta na neman shafe addinin Islama a yankin.
A kan haka ne babban editan Sashen Hausa na Muryar Amurka Aliyu Mustaphan Sokoto ya tattauna da Bahaushen Sinawa Mallam Audu Bako Li na gidan rediyon China. Aliyu Mustaphan Sokoto ya tambayi Audu Bako Li, wai da gaske ne hukumomin kasar Sin sun hana Musulmin yankin Xinjiang yin azumin watan Ramadan?
Hukumomin kasar Sin sun bada hujjar cewa sun dauki matakin haramta yin azumin ne da nufin kare lafiyar dalibai, su kuma ma'aikatan gwamnati sun hana su yin azumi ne don su tabbatar da cewa gwamnati ba ta goyon bayan kowane irin addini.
Amma Musulmi 'yan kabilar Uighur mazauna lardin Xinjiang sun ce matakan tsaurin da hukumomin Sin su ka dauka sun bayar da akasin sakamako saboda mazauna yankin sun dage da azumi fiye da kowane lokaci, har ma gadara suke yiwa da zuwa Masallatai da kuma karatun AlQura'ani duk da dokokin da gwamnatin ta kafa na takura mu su da takaita mu su yin wadannan abubuwa mahimmai a addinin Islama, zuwa Masallaci Sallah, da karanta AlQura'ani.