Gwamnatin Habasha Ta Ayyana Tsagaita Wuta a Yankin Tigray

TIGRAY

Gwamnatin Habasha ta ayyana tsagaita wuta a yankin Tigray, yayinda tsohuwar jam’iyar da ke mulki a kasar da dakarunta suka shiga Mekelle babban birnin yankin.

Gwamnatin Habasha ta ayyana tsagaita wuta a yankin Tigray, yayinda tsohuwar jam’iyar da ke mulki a kasar da dakarunta suka shiga Mekelle babban birnin yankin, lamarin da ya sa al’ummar yankin famtsama tituna suna murna

Gwamnatin kasar Habasha ta sanar a kafar sadarwar kasar Jiya Litinin cewa, za ta daina musayar wuta ba tare da bata lokaci ba, biyo bayan shafe watanni takwas ana rikici a yankin.

Wakilin Muryar Amurka a Mekelle ya ce ba su ga sojojin gwamnati a birnin ba tun ranar Lahadi.

Dakarun ‘yan tawaye daga jam’iyar ‘yantar da al’ummar Tigray –TPLF da ke mulki a yankin, sun sanar a tashar radiyon jam’iyar cewa, dakarunsu sun shiga Mekelle.