Gwamnatin Filato Za Ta Fara Rajistan Masu Keke NAPEP

Mashinan Keke-Napep (Facebook/PLSG)

Komishinan Sufuri a jihar Filato, Davou Gyang Jatau yace gwamnati za ta farfado da dokar da zata tantance masu amfani da kekunan NAPEP da wadanda suka mallake su, ta hanyar amfani da na'urori na zamani. 

A shekara ta dubu biyu da goma sha biyu ne, gwamantin jihar Filato ta dakatar da ayyukan zirga-zirgar babura a cikin birnin Jos, saboda yawan hadura da rasa rayuka dake afkuwa.

Majalisar Dokokin jihar Filato na wancan lokaci ta amince da amfani da motocin tasi da babura masu kafa uku, da aka fi sani da "keke NAPEP", don yin sufuri a cikin kwaryar birnin Jos.

To sai dai a cikin 'yan shekarun nan, ayyukan assha da wadansu batagari ke aikatawa da keke NAPEP ya sanya gwamnatin farfado da dokar da zata tantance masu amfani da kekunan da wadanda suka mallake su, ta hanyar amfani da na'urori na zamani.

Kwamishinan Sufuri a jihar Filato, Davou Gyang Jatau yace gwamnati ta dauki matakin tantancewar ne don tsaron lafiyar al'umma da dukiyoyinsu.

Malam Michael Magaji, Shugaban kamfanin GIOPAT, da zata gudanar da aikin tantance kekunan, yace rajistan da za'a yi zai kunshi taimako daga bankuna.

Hajiya Fatima Idris Gindiri daya daga cikin wadanda ke sayen kekuna suna baiwa matasa a bashi, tace sun yi na'am da matakin tantancewar don tsabtace harkar kasuwancinsu.

Gwamnatin jihar Filato ta baiwa kamfanin kwanaki talatin ne kachal, su yi rajista wa dubban keke NAPEP dake aiki a fadin jhar.

Saurari rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Filato Za Ta Fara Rajistan Masu Keke NAPEP